1 Yuni 2020 - 07:35
Libya: Dakarun Halifa Haftar Sun Cilla Rokoki Kan Birnin Tripoli

Dakarun Halifa Haftar, wadanda suke kiran kansu sojojin kasar Libya sun cilla makaman roka a kan birnin Tripoli babban birnin kasar a jiya Lahadi da yamma.

Ehlibeyt (as) Haber Ajansı ABNA - Dakarun Halifa Haftar, wadanda suke kiran kansu sojojin kasar Libya sun cilla makaman roka a kan birnin Tripoli babban birnin kasar a jiya Lahadi da yamma.

Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto majiyar gwamnatin hadin kan kasa ta kasar Libya, wacce kuma kasashen duniya suka amince da samuwarta, tana cewa rikokin sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 5 da kuma raunata wasu 12.

Mayakan Halifa Haftar dai, wadanda suke iko da gabacin kasar Libya, sannan suke samun goyon bayan kasashen Masar, Saudiya da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa sun mamaye yankuna da dama na kasar.

Sai kuma a ranar 4 ga watan Afrilun shekara ta 2019 dakarun na Halifa Haftar suka farwa birnin Tripoli da yaki da nufin kwace shi daga hannun gwamnatin hadin kan kasa wacce Fa’iza Sarraaj yake jagoranta.

Ya zuwa yanzu dai an kashe mutane kimani 1500 a bangarorin biyu, sannan wasu 6000 kuma sun sami raunuka. Har’ila yau wasu dubu 150 sun kauracewa gidajensu.


/129